11
Zofar
1 Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
2 “Duk surutun nan ba za a amsa maka ba?
Ko mai surutun nan marar laifi ne?
3 Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru?
Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?
4 Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne
kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’
5 Da ma Allah zai yi magana,
yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba
6 yă kuma buɗe maka asirin hikima,
gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu.
Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.
7 “Ko za ka iya gane al’amuran Allah?
Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?
8 Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi?
Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani?
9 Tsayinsu ya fi tsawon duniya
da kuma fāɗin teku.
10 “In ya zo ya kulle ka a kurkuku
ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?
11 Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya;
kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?
12 Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima
kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.
13 “Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka,
ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,
14 in ka kawar da zunubin da yake hannunka,
ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba
15 shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba;
za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba.
16 Ba shakka za ka manta da wahalolinka,
za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa.
17 Rayuwarka za tă fi hasken rana haske,
duhu kuma zai zama kamar safiya.
18 Za ka zauna lafiya, domin akwai bege;
za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.
19 Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro,
da yawa za su zo neman taimako a wurinka.
20 Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba,
kuma ba za su iya tserewa ba;
begensu zai zama na mutuwa.”