Zabura 20
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala;
bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki
yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.
Bari yă tuna da dukan sadakokinka
yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa.
Sela
Bari yă biya maka bukatan ranka
yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara
mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu.
 
Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.
 
Yanzu na san cewa,
Ubangiji yakan cece shafaffensa.
Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki
da ikon ceto na hannun damansa.
Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai,
amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.
Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi,
amma mu za mu tashi mu tsaya daram.
Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki!
Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!