Zabura 31
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka;
kada ka bari in taɓa shan kunya;
ka cece ni cikin rahamarka.
2 Ka juye kunnenka gare ni,
ka zo da sauri ka cece ni;
ka zama dutsen mafakata,
mafaka mai ƙarfi na cetona.
3 Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata,
saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.
4 Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini,
gama kai ne mafakata.
5 Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna;
ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.
6 Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza;
na dogara ga Ubangiji.
7 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikin ƙaunarka,
gama ka ga azabata
ka kuma san wahalar raina.
8 Ba ka ba da ni ga abokin gāba ba
amma ka sa ƙafafuna a wuri mai sarari.
9 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa;
idanuna sun gaji da baƙin ciki,
raina da jikina sun tafke tilis.
10 Baƙin ciki ya rufe raina
shekaruna sun cika da nishi;
ƙarfina ya karai saboda azaba,
ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis.
11 Saboda dukan abokan gābana,
Na zama tamƙar abin reni na maƙwabtana;
na zama abin tsoro ga abokaina,
waɗanda suka gan ni a titi sukan gudu daga gare ni.
12 An manta da ni sai ka ce na mutu;
na zama kamar fasasshen kasko.
13 Gama nakan ji raɗe-raɗen mutane masu yawa;
akwai tsoro a kowane gefe;
suna ƙulla maƙarƙashiya a kaina
suna shirya su ɗauke raina.
14 Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji;
na ce, “Kai ne Allahna.”
15 Lokutana suna a hannuwanka;
ka cece ni daga abokan gābana
da kuma daga waɗanda suke fafara ta.
16 Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka;
ka cece ni da ƙaunarka marar ƙarewa.
17 Kada ka bari in sha kunya, ya Ubangiji,
gama na yi kuka gare ka;
amma bari mugaye su sha kunya
su kuma kwanta shiru a cikin kabari.
18 Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu,
gama da fariya da reni
suna magana da girman kai a kan adalai.
19 Alherinka da girma yake,
wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka,
wanda ka mayar a gaban mutane
a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.
20 Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su
daga makircin mutane;
a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya
daga harsuna masu zagi.
21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni
sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni.
22 Cikin tsorona na ce,
“An yanke ni daga gabanka!”
Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai
sa’ad da na kira gare ka don taimako.
23 Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa!
Ubangiji yakan adana amintattu,
amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke.
24 Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,
dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.