Zabura 38
Zabura ta Dawuda. Roƙo ne.
Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka
ko ka hore ni cikin hasalarka.
Gama kibiyoyinka sun soke ni,
hannunka kuma ya fāɗo a kaina.
Saboda hasalarka babu lafiya a jikina;
ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.
Laifofina sun mamaye ni
kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.
 
Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari
saboda wawancina na zunubi.
An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni;
dukan yini ina ta kuka.
Bayana yana fama da zazzaɓi;
babu lafiya a jikina.
Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni;
ina nishi da wahala a cikin zuciyata.
 
Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji;
ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
10 Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare,
har ma haske ya rabu da idanuna.
11 Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna;
maƙwabtana ba sa zuwa kusa.
12 Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu,
waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni;
yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.
 
13 Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji,
kamar bebe, wanda ba ya iya buɗe bakinsa.
14 Na zama kamar mutumin da ba ya ji,
wanda bakinsa ba ya iya ba da amsa.
15 Na dogara gare ka, ya Ubangiji;
za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.
16 Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina
ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.”
 
17 Gama ina gab da fāɗuwa,
kuma cikin azaba nake kullum.
18 Na furta laifina;
na damu da zunubina.
19 Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi;
waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa.
20 Waɗanda suke sāka alherina da mugunta,
suna cin zarafina
sa’ad da nake bin abin da yake daidai.
 
21 Ya Ubangiji, kada ka yashe ni;
kada ka yi nesa da ni, ya Allahna.
22 Zo da sauri ka taimake ni,
Ya Ubangiji Mai Cetona.