Zabura 65
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa.
Yabo ya dace* Ko kuwa kan jira; ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba. da kai, ya Allah, a Sihiyona;
a gare ka za mu cika alkawuranmu
Ya kai wanda yake jin addu’a
a gare ka dukan mutane za su zo.
Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu,
ka gafarta Ko kuwa ka yi kafara domin laifofinmu.
Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa
ka kawo kusa don su zauna a filayenka!
Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka,
na haikalinka mai tsarki.
 
Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci,
Ya Allah Mai Cetonmu,
begen dukan iyakar duniya
da kuma na tekuna masu nesa,
wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka,
bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,
wanda ya kwantar da rurin tekuna,
rurin raƙumansu,
da kuma tumbatsar al’ummai.
Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka;
inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe
kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.
 
Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa;
kana azurta ta a yalwace.
Rafuffukan Allah sun cika da ruwa
don su ba mutane hatsi,
don haka ne ka ƙaddara. Ko kuwa don haka ne ka shirya ƙasar
10 Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta;
ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.
11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka,
amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.
12 Makiyayan hamada sun cika har suna zuba;
tuddai sun rufu da murna.
13 Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna
kwari kuma sun cika da hatsi;
suna sowa don farin ciki.

*Zabura 65:1 Ko kuwa kan jira; ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba.

Zabura 65:3 Ko kuwa ka yi kafara domin

Zabura 65:9 Ko kuwa don haka ne ka shirya ƙasar