Zabura 110
Ta Dawuda. Zabura ce.
Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana,
sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka.”
 
Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona
za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.
Rundunarka za su so yin yaƙi
a ranarka ta yaƙi.
Saye cikin ɗaukaka mai tsarki,
daga cikin ciki na safiya
za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.* Ko kuwa / samarinka za su zo gare ka kamar raba
 
Ubangiji ya rantse
ba zai kuma canja zuciyarsa ba,
“Kai firist ne har abada,
bisa ga tsarin Melkizedek.”
 
Ubangiji yana a hannun damanka;
zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.
Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki
yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.
Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya;
saboda haka zai ɗaga kansa sama.

*Zabura 110:3 Ko kuwa / samarinka za su zo gare ka kamar raba