Zabura 138
Ta Dawuda.
1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
a gaban “alloli” zan rera yabo.
2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki
zan kuma yabi sunanka
saboda ƙaunarka da amincinka,
saboda ka ɗaukaka a bisa kome
sunanka da kuma maganarka.
3 Sa’ad da na kira, ka amsa mini;
ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.
4 Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji,
sa’ad da suka ji maganganun bakinka.
5 Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji,
gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.
6 Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu,
amma tun da nesa ya san masu girman kai.
7 Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala,
kana kiyaye raina;
ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana,
da hannunka na dama ka cece ni.
8 Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;
ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,
kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.