Zabura 141
Zabura ta Dawuda.
1 Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri.
Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.
2 Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa;
bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.
3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji;
ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
4 Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu,
ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka
tare da mutane masu aikata mugunta;
kada ka bari in ci abincinsu.
5 Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne;
bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina.
Kaina ba zai ƙi shi ba,
duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.
6 Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse,
mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.
7 Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa,
haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.”
8 Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka;
a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.
9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini,
daga tarkon da mugaye suka sa.
10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu,
amma bari ni in zo in wuce lafiya.