1 Tarihi
1
Rubutaccen tarihi daga Adamu zuwa Ibrahim
Zuwa ’Ya’yan Nuhu Maza
1 Adamu, Set, Enosh,
2 Kenan, Mahalalel, Yared,
3 Enok, Metusela, Lamek, Nuhu.
4 ’Ya’yan Nuhu maza su ne,* Seftuwajin; Ibraniyanci ba su da ’Ya’yan Nuhu maza. Shem, Ham da Yafet.
Mutanen Yafet
5 ’Ya’yan† ’Ya’ya suna iya nufin zuriya Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 6-10, 17 da 20. Yafet maza su ne,
Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.
6 ’Ya’yan Gomer maza su ne,
Ashkenaz, Rifat‡ Yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da na Bulget (dubi kuma Seftuwajin da Far 10.3); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Difat da Togarma.
7 ’Ya’yan Yaban maza su ne,
Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
Mutanen Ham
8 ’Ya’yan Ham maza su ne,
Kush, Masar§ Wato, Masar; haka ma a aya ta 11. Fut da Kan’ana.
9 ’Ya’yan Kush maza su ne,
Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.
’Ya’yan Ra’ama maza su ne,
Sheba da Dedan
10 Kush shi ne mahaifin* Mahaifi na iya nufin kaka ko wanda ya riga Ko kuwa wanda yake tushe; haka ma a ayoyi 11, 13, 18 da 20.
Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.
11 Masar shi ne mahaifin
Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa, 12 Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa.
13 Kan’ana shi ne mahaifin
Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa, 14 Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa 15 Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, 16 Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa.
Semiyawa
17 ’Ya’yan Shem maza su ne,
Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
’Ya’yan Aram maza su ne,
Uz, Hul, Geter da Meshek.
18 Arfakshad shi ne mahaifin Shela,
Shela kuwa shi ne mahaifin Eber.
19 Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.
Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan.
20 Yoktan shi ne mahaifin
Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera 21 Hadoram, Uzal, Dikla, 22 Ebal, Abimayel, Sheba, 23 Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
Zuriyar Shem
24 Shem, Arfakshad,† Da Ibraniyanci; waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin suna da Arfakshad, Kainan (dubi kuma sharhi a Far 11.10). Shela,
25 Eber, Feleg, Reyu
26 Serug, Nahor, Tera
27 da Abram (wato, Ibrahim).
Iyalin Ibrahim
28 ’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel.
Zuriyar Hagar
29 Waɗannan su ne zuriyarsu.
Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, 30 Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema 31 Yetur, Nafish da Kedema.
Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza.
Zuriyar Ketura
32 ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne,
Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.
’Ya’yan Yokshan maza su ne,
Sheba da Dedan.
33 ’Ya’yan Midiyan maza su ne,
Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a.
Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.
Zuriyar Saratu
34 Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku.
’Ya’yan Ishaku maza su ne,
Isuwa da Isra’ila.
’Ya’yan Isuwa maza
35 ’Ya’yan Isuwa maza, su ne,
Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora
36 ’Ya’yan Elifaz maza su ne,
Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz,
da Timna wanda aka haifa wa Amalek.‡ Waɗansu rubuce-rubucen hannun Seftuwajin (dubi Far 36.12); Ibraniyanci yana da Gatam, Kenaz, Timna da Amalek
37 ’Ya’yan maza Reyuwel su ne,
Nahat, Zera, Shamma da Mizza.
Mutanen Seyir a Edom
38 ’Ya’yan Seyir maza su ne,
Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.
39 ’Ya’yan Lotan maza su ne,
Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan.
40 ’Ya’yan Shobal maza su ne,
Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
’Ya’yan Zibeyon maza su ne,
Aiya da Ana.
41 Ɗan Ana shi ne,
Dishon.
’Ya’yan Dishon maza su ne,
Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
42 ’Ya’yan Ezer maza su ne,
Bilhan, Za’aban da Ya’akan.
’Ya’yan Dishan maza su ne,
Uz da Aran.
Masu mulkin Edom
43 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta.
Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.
44 Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.
45 Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.
46 Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.
47 Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.
48 Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.
49 Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.
50 Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab. 51 Hadad shi ma ya mutu.
Manyan Edom su ne,
Timna, Alwa, Yetet 52 Oholibama, Ela, Finon 53 Kenaz, Teman, Mibzar, 54 Magdiyel da Iram.
Waɗannan su ne manyan Edom.
*1:4 Seftuwajin; Ibraniyanci ba su da ’Ya’yan Nuhu maza.
†1:5 ’Ya’ya suna iya nufin zuriya Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 6-10, 17 da 20.
‡1:6 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da na Bulget (dubi kuma Seftuwajin da Far 10.3); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Difat
§1:8 Wato, Masar; haka ma a aya ta 11.
*1:10 Mahaifi na iya nufin kaka ko wanda ya riga Ko kuwa wanda yake tushe; haka ma a ayoyi 11, 13, 18 da 20.
†1:24 Da Ibraniyanci; waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin suna da Arfakshad, Kainan (dubi kuma sharhi a Far 11.10).
‡1:36 Waɗansu rubuce-rubucen hannun Seftuwajin (dubi Far 36.12); Ibraniyanci yana da Gatam, Kenaz, Timna da Amalek