6
Solomon ya gina haikali
1 A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.
2 Haikalin da Sarki Solomon ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu talatin ne. 3 Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma. 4 Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin. 5 A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe. 6 Fāɗin ɗakunan ƙasa, kamu biyar ne, fāɗin ɗakunan tsakiya, kamu shida ne, fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa, kamu bakwai ne. Ya yi bangaye kewaye a waje da haikalin don kada a sa wani abu a bangayen haikali.
7 A yin ginin haikalin, duwatsun da aka fafe ne kaɗai daga wurin fafe duwatsu aka yi amfani da su, ba a ji karar guduma ko gizago, ko wani abin da aka yi da ƙarfe a wurin ginin haikali yayinda ake gina shi ba.
8 Ƙofar zuwa ɗakunan ƙasa tana gefen kudu na haikalin; akwai matakai da suka bi zuwa hawa na tsakiya, daga can kuma matakan sun wuce zuwa hawa na uku. 9 A haka ya gina haikalin ya kuma gama shi, ya jinƙe shi da manyan katakai da kuma katakan al’ul. 10 Ya kuma gina ɗakunan gefe duka a gefen haikalin. Tsayin kowanne, kamu biyar ne, aka haɗa su da haikalin da manyan katakan al’ul.
11 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Solomon ta ce, 12 “Game da wannan haikalin da kake ginawa, in ka bi ƙa’idodina, ka cika farillaina, ka kiyaye dukan umarnaina, ka kuma yi biyayya da su, zan cika alkawarin da na yi wa mahaifinka Dawuda ta wurinka. 13 Zan kuma zauna a cikin Isra’ilawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”
14 Saboda haka Solomon ya gina haikalin ya kuma gama shi.
15 Ya rufe bangon ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama, ya kuma rufe daɓen da katakan itacen fir. 16 Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi a can ƙuryar haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama. 17 Tsawon babban zaure a gaban wannan ɗaki, kamu arba’in ne. 18 An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
19 Ya shirya wuri mai tsarki na ciki can cikin haikali don yă sa akwatin alkawarin Ubangiji a can. 20 Tsawon wuri mai tsarki na ciki kamu ashirin, fāɗin kamu ashirin, tsayin kuma kamu ashirin. Ya dalaye cikin da zinariya zalla, ya kuma dalaye bagade al’ul ɗin. 21 Solomon ya rufe cikin haikalin da zinariya zalla, ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban wuri mai tsarki na ciki, wanda aka dalaye da zinariya. 22 Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya.
23 A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma. 24 Fiffike ɗaya na kerub na fari tsawonsa kamu biyar ne, ɗayan fiffike kuma kamu biyar, kamu goma daga ƙarshen fiffike zuwa ƙarshen fiffike. 25 Kerub na biyun shi ma kamu goma ne, gama kerubobi biyun sun yi kama da juna a girma da kuma siffa. 26 Tsayin kowane kerub kamu goma ne. 27 Ya ajiye kerubobin a ɗaki na can cikin haikalin, da fikafikansu a buɗe. Fiffiken kerub ɗaya ya taɓa bango guda, yayinda fiffiken ɗayan ya taɓa ɗayan bangon, kuma fikafikansu sun taɓa juna a tsakiyar ɗakin. 28 Ya dalaye kerubobin da zinariya.
29 A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu. 30 Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya.
31 Don ƙofar shiga wuri mai tsarki na ciki kuwa, ya yi ƙofofin katakon zaitun da madogarai masu gefe biyar. 32 A kan ƙofofin katakan zaitun kuwa ya zāzzāna kerubobi, itatuwa dabino, da furanni buɗaɗɗu, ya kuma dalaye kerubobin, da kuma itatuwan dabinon da zinariya. 33 Haka ma ya yi madogarai masu gefe huɗu na katakon zaitun don ƙofar shiga zuwa babban zaure. 34 Ya yi ƙofofi biyu na itacen fir, kowanne yana da shafi biyu da suke juyewa a maɗaurai. 35 Ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da kuma furanni buɗaɗɗu a kansu, ya kuma dalaye su da zinariyar da aka buga daidai a kan sassaƙa.
36 Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.
37 An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif. 38 A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.