24
Dawuda ya bar Shawulu da rai
Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.” Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji.
Da Shawulu ya isa inda ake ajiye garken tumaki a bakin hanya inda akwai kogo, sai ya shiga ciki kogon don yă yi bayan gari. Dawuda da mutanensa kuwa suna can zaune a ƙurewar kogon. Mutanen Dawuda suka ce, wannan rana ce Ubangiji ya yi magana ya ce maka, “Zan ba da maƙiyinka a hannunka domin ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sai Dawuda ya tashi a hankali ya je ya yanke shafin rigar Shawulu.
Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu. Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.” Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa.
Daga baya Dawuda ya fita daga kogon sai ya kira Shawulu ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki!” Da Shawulu ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. Ya ce wa Shawulu, “Me ya sa kake saurari mutanen da suke cewa, ‘Dawuda ya dāge yă cuce ka’? 10 Yau ka ga da idonka yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a cikin kogon nan. Waɗansu sun ce mini in kashe ka, amma na bar ka, na ce, ‘Ba zan sa hannuna a kan shugabana ba, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.’ 11 Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina. 12  Ubangiji zai shari’anta tsakanina da kai. Ubangiji zai sāka mini laifin da ka yi mini, amma ni kam ba zan taɓa ka ba. 13 Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba.
14 “Wane ne sarkin Isra’ila, ka fito kake bi? Wa kake kora? Kana bin mataccen kare ko kuɗin cizo? 15  Ubangiji yă zama alƙali, yă yi shari’a tsakanina da kai, bari Ubangiji yă duba, yă tsaya mini, yă nuna ba ni da laifi.”
16 Da Dawuda ya gama wannan magana, sai Shawulu ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Sai ya fasa da kuka. 17 Ya ce, “Ka fi ni gaskiya, ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta. 18 Ga shi yanzu ka faɗa mini alherin da ka yi mini. Ubangiji ya bashe ni a hannunka amma ba ka kashe ni ba. 19 In mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi yă tafi lafiya ba tare da yin masa rauni ba? Ubangiji yă sāka maka, gama ka nuna mini alheri a yau. 20 Na sani tabbatacce za ka zama sarki. Masarautar Isra’ila za tă kahu a hannunka. 21 Yanzu ka rantse mini da Ubangiji cewa ba za ka hallaka zuriyarta ko ka share sunana daga iyalin mahaifina ba.”
22 Sai Dawuda ya rantse wa Shawulu. Sa’an nan Shawulu ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka haura zuwa wurin ɓuya.