10
Dawuda ya ci Ammonawa da yaƙi
1 Ana nan sai sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa Hanun kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. 2 Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan yi wa Hanun ɗan Nahash alheri kamar yadda mahaifinsa ya yi mini.” Saboda haka sai Dawuda ya aiki jakadu su yi masa ta’aziyyar mutuwar mahaifinsa.
Sa’ad da mutanen Dawuda suka isa ƙasar Ammonawa, 3 sai manyan mutanen Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko da jakadu su kawo maka ta’aziyya? Ai, wayo ya yi don yă ga asirin birninmu, yă san ƙarfinmu, yă kuma ci mu da yaƙi.” 4 Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda ya aske rabin gemun kowannensu, ya yayyage rigunarsu daidai ɗuwawu, sa’an nan ya sallame su.
5 Sa’ad da aka gaya wa Dawuda game da wannan, sai ya aiki manzanni su taryi waɗannan mutanen da aka ci mutuncinsu, gama an wulaƙanta su ƙwarai. Sai sarki ya ce musu, “Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya sāke girma, sa’an nan ku dawo.”
6 Da Ammonawa suka gane cewa Dawuda ya ji fushi da su sosai saboda abin da suka yi, sai suka yi hayar sojojin ƙasar Arameyawa dubu ashirin daga Bet Rehob da Aram-Zoba, suka kuma yi hayar sarkin Ma’aka tare da mutum dubu ɗaya, suka kuma yi hayar maza dubu goma sha biyu daga Tob.
7 Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi. 8 Ammonawa suka fita suka ja dāgār yaƙi a ƙofar shiga birninsu, yayinda Aram-Zoba, da na Rehob, da mutane Tob, da kuma na Ma’aka, suka ja tasu dāgār a karkara.
9 Yowab ya ga cewa an ja masa dāgār yaƙi gaba da baya; saboda haka sai ya zaɓi waɗansu shahararrun sojoji cikin Isra’ila, ya sa su gabza da Arameyawa. 10 Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin Abishai ɗan’uwansa, ya sa su gabza da Ammonawa. 11 Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ƙarfina, sai ku kawo mini gudummawa; amma in Ammonawa suka fi ƙarfinku, sai mu kawo muku gudummawa. 12 Ku yi ƙarfin hali, mu kuma yi yaƙi da ƙarfin zuciya saboda mutanenmu da kuma birane Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da yake da kyau a idanunsa.”
13 Sa’an nan Yowab da rundunar da take tare da shi suka ci gaba don su gabza da Arameyawa, Arameyawa kuwa suka gudu a gabansa. 14 Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa.
15 Bayan Arameyawa suka ga Isra’ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke tattara kansu. 16 Hadadezer sarkin Zoba ya aika a kawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yuferites. Suka iso Helam a ƙarƙashin shugabancin Shobak, shugaban dukan sojojin Hadadezer.
17 Da aka gaya wa Dawuda wannan, sai ya tattara dukan Isra’ila, ya ƙetare Urdun, ya je Helam. Arameyawa suka ja dāgār yaƙinsu, suka kara da Dawuda. 18 Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can. 19 Sa’ad da dukan sarakuna waɗanda suke abokan tarayya na Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa, suka kuma zama bayinsu.
Wannan ya sa Arameyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudummawa.