8
Jerin shugabannin iyalan da suka dawo tare da Ezra
Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes.
 
Daga zuriyar Finehas,
Gershom ne shugaba;
daga zuriyar Itamar,
Daniyel ne shugaba;
daga zuriyar Dawuda,
Hattush ɗan zuriyar Shekaniya ne shugaba,
daga zuriyar Farosh,
Zakariya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 150;
daga Fahat-Mowab,
Eliyehoyenai ɗan Zerahiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 200;
daga zuriyar Zattu,
Shekaniya ɗan Yahaziyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 300;
daga zuriyar Adin,
Ebed ɗan Yonatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 50;
daga zuriyar Elam,
Yeshahiya ɗan Ataliya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 70;
daga zuriyar Shefatiya,
Zebadiya ɗan Mika’ilu ne shugaba, tare da shi akwai mutum 80;
daga iyalin Yowab,
Obadiya ɗan Yehiyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 218;
10 daga Bani,
Shelomit ɗan Yosifiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 160;
11 daga Bebai,
Zakariya ɗan Bebai ne shugaba, tare da shi akwai mutum 28;
12 daga iyalin Azgad,
Yohanan ɗan Hakkatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 110;
13 zuriya ta Adonikam ne suka zo daga ƙarshe,
sunayensu kuwa su ne Elifelet, Yehiyel da Shemahiya, tare da su akwai mutum 60;
14 daga zuriyar Bigwai,
Uttai da Zakkur ne shugabanni, tare da su akwai mutum 70.
Dawowa Urushalima
15 Na kuma tattara su a bakin rafi wanda yake gangarawa zuwa Ahawa, muka kafa sansani a can kwana uku. Da na bincika cikin mutane da firistoci, sai na tarar babu Lawiyawa. 16 Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne. 17 Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da ’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu. 18 Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da ’ya’yansa da kuma ’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne. 19 Suka kuma aika da Hashabiya tare da Yeshahiya daga zuriyar Merari, da ’yan’uwansu da kuma ’ya’yansu, su kuma mutum 20 ne. 20 Sun kuma kawo masu aiki a haikali mutum 220, ƙungiyar da Dawuda da abokan aikinsa suka keɓe don su taimaki Lawiyawa aiki. Duk aka rubuta waɗannan da sunayensu.
21 A can, a bakin rafin Ahawa, na sa mu yi azumi, domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu kuma roƙe shi yă kiyaye mana hanya, da mu da ’ya’yanmu da kayanmu duka. 22 Na ji kunya in roƙi sarki yă haɗa mu da sojoji da masu dawakai don su yi mana rakiya su kāre mu daga magabta a kan hanya, gama mun ce wa sarki, “Alherin Allah yana tare da duk wanda yake dogara gare shi, amma kuma fushinsa yana kan duk wanda ya juya masa baya.” 23 Saboda haka sai muka yi azumi, muka kai roƙonmu a wurin Allah, ya kuwa amsa mana.
24 Sai na keɓe manyan firistoci guda goma sha biyu tare da Sherebiya, Hashabiya da kuma ’yan’uwansu guda goma. 25 Na auna musu zinariya da azurfa, da kwanoni waɗanda sarki da mashawartansa, da sauran abokan aikinsa, da Isra’ilawan da suke can suka bayar domin haikalin Allahnmu. 26 Na auna musu talenti 650 na azurfa, talenti ɗari na kwanonin azurfa, talenti 100 na zinariya, 27 kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya.
28 Na ce masa, “Ku da kayan nan tsarkaka ne ga Ubangiji. Azurfa da zinariya ɗin, bayarwa ce ta yardar rai ga Ubangiji, Allah na kakanninku. 29 Ku lura da su da kyau har sai kun isa Urushalima. Ku auna su a shirayin haikalin Ubangiji a Urushalima, a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai na Isra’ila.” 30 Sa’an nan sai firistoci, da Lawiyawa suka karɓi azurfa da zinariya da kuma tsarkakan kwanonin da aka auna don a kai haikalin Allahnmu a Urushalima.
31 A rana ta goma sha biyu ga watan farko, muka tashi daga bakin rafin Ahawa don mu tafi Urushalima. Alherin Allahnmu yana tare da mu, ya kuma kāre mu daga magabta da ’yan fashi. 32 Muka iso Urushalima, inda muka huta kwana uku.
33 A rana ta huɗu muka tafi haikalin Allah, muka auna azurfa, da zinariya, da tsarkakan kwanonin, muka ba Meremot ɗan Uriya firist, da Eleyazar ɗan Finehas yana tare da shi, da kuma Lawiyawan nan, wato, Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi. 34 Aka yi lissafi aka auna kome aka tarar yana nan daidai, aka kuma rubuta yawan nauyin a lokacin.
35 Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida, ’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji. 36 Suka kuma kai saƙon sarki zuwa ga wakilansa, da kuma gwamnoni na Kewayen Kogin Yuferites waɗanda suka taimaki mutane da kuma gidan Allah.