14
1 Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai;
zai sāke zaɓi Isra’ila
yă kuma zaunar da su a ƙasarsu.
Baƙi ma za su zo su zauna tare da su
su haɗa kai da gidan Yaƙub.
2 Al’ummai za su ɗauke su
su kuma kawo wurin da yake nasu.
Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai
a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji.
Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu
su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
3 A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta, 4 za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a.
Mai danniya ya zo ga ƙarshe!
Dubi yadda fushinsa ya ƙare!
5 Ubangiji ya karye sandar mugaye,
sandan mulkin masu mulki,
6 wanda cikin fushi ya kashe mutane
da bugu marar ƙarewa,
kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai
da fushi ba ƙaƙƙautawa.
7 Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama;
sun ɓarke da waƙa.
8 Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon
suna murna a kanka suna cewa,
“Yanzu da aka ƙasƙantar da kai,
babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”
9 Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya
don yă sadu da kai a zuwanka;
yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka,
dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya;
ya sa suka tashi daga kujerun sarauta,
dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai.
10 Duk za su amsa,
za su ce maka,
“Ashe kai ma raunana ne, kamar mu;
ka zama kamar mu.”
11 An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari,
tare da surutan garayunka;
tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka
tsutsotsi kuma suka rufe ka.
12 Yaya aka yi ka fāɗo daga sama
Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba!
An fyaɗa ka da ƙasa,
kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
13 Ka yi tunani a ranka ka ce,
“Zan hau zuwa sama;
zan ɗaga kursiyina
sama da taurarin Allah;
zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro,
a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.* Ko kuwa arewa; Da Ibraniyanci Zafon
14 Zan haura can bisa gizagizai;
zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”
15 Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari,
zuwa zurfafan rami.
16 Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido,
suna tunani abin da zai same ka.
“Wannan mutumin ne ya girgiza duniya
ya kuma sa mulkoki suka razana,
17 mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada,
wanda ya tumɓuke biranenta
bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”
18 Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace,
kowa a kabarinsa.
19 Amma an jefar da kabarinka
kamar reshen da aka ƙi;
an rufe ka da waɗanda aka kashe,
tare da waɗanda aka soke da takobi,
waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami.
Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,
20 ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba,
gama ka hallaka ƙasarka
ka kuma kashe mutanenka.
Ba za a ƙara ambaci
zuriyarka masu aikata mugunta ba.
21 A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza
saboda zunuban kakanninsu;
kada a reno su su gāji ƙasar
su cika duniya da biranensu.
22 “Zan yi gāba da su,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta,
’ya’yanta da zuriyarta,”
in ji Ubangiji.
23 “Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi
da kuma fadama;
zan share ta da tsintsiyar hallaka,”
Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
Annabci a kan Assuriya
24 Ubangiji Maɗaukaki ya rantse,
“Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance,
kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
25 Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata;
a kan duwatsuna zan tattake shi.
Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena,
a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
26 Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya;
wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
27 Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi?
Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
Annabci a kan Filistiyawa
28 Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu.
29 Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa,
cewa sandar da ta buge ku ta karye;
daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso,
’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.
30 Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo,
mabukata kuma za su kwana lafiya.
Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa;
za tă kashe naka da suka rage da rai.
31 Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni!
Ku razana, dukanku Filistiyawa!
Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa,
kuma babu matsorata a cikin sojojinsa.
32 Wace amsa ce za a bayar
wa jakadun wannan al’umma?
“Ubangiji ya kafa Sihiyona,
kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”