30
Kaiton al’umma mai tayarwa
1 “Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,”
in ji Ubangiji,
“ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba,
suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba,
suna jibga zunubi a kan zunubi;
2 waɗanda suka gangara zuwa Masar
ba tare da sun nemi shawarata;
waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna,
don neman inuwar mafakar Masar.
3 Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya,
inuwar Masar za tă jawo muku kunya.
4 Ko da yake suna da shugabanni a Zowan
kuma jakadunsu sun iso Hanes,
5 kowa zai sha kunya
saboda mutanen da ba su da amfani gare su,
waɗanda ba sa taimako ko amfani,
sai dai jawo kunya da da-na-sani.”
6 Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa,
Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari
inda zakoki da zakanya,
inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke,
jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna,
dukiyarsu a kan raƙuma,
zuwa ƙasan nan marar riba,
7 zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne.
Saboda haka na yi mata laƙabi
Rahab Marar Yin Kome.
8 Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo,
ka rubuta shi a kan littafi,
cewa kwanaki suna zuwa
zai zama madawwamin shaida.
9 Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu,
’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.
10 Sukan ce wa masu gani,
“Kada ku ƙara ganin wahayi!”
Ga annabawa kuwa sukan ce,
“Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai!
Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai,
ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.
11 Ku bar wannan hanya,
ku tashi daga wannan hanya,
ku kuma daina kalubalantarmu
da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!”
12 Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa,
“Saboda haka kun ƙi wannan saƙo,
kuka dogara ga aikin kama-karya
kuka kuma dogara ga yin ruɗu,
13 wannan zunubi zai zama muku
kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa,
da zai rushe nan da nan, ba tsammani.
14 Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu,
ya ragargaje ƙaf
har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga
don ɗiba garwashin wuta
ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.”
15 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa,
“Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake,
cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku,
amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.
16 Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’
Saboda haka za ku gudu!
Kun ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri mu gudu.’
Saboda haka masu fafararku za su fi ku gudu!
17 Dubu za su gudu
don barazanar mutum guda;
da jin barazanar mutane biyar
dukanku za ku yi ta gudu
sai an bar ku
kamar sandar tuta a kan dutse,
kamar tuta a kan tudu.”
18 Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;
ya tashi don yă nuna muku jinƙai.
Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.
Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!
19 Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku. 20 Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su. 21 Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.” 22 Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”
23 Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya. 24 Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali. 25 A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo. 26 Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.
27 Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa,
tare da fushi mai ƙuna da kuma baƙin hayaƙi;
leɓunansa sun cika da fushi,
harshensa kuma wuta ce mai cinyewa.
28 Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu
yana tashi har zuwa wuya.
Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka;
yakan sa a muƙamuƙan mutane
linzamin da zai jagorance su su kauce.
29 Za ku kuma rera
kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki;
zukatanku za su yi farin ciki
kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa
zuwa dutsen Ubangiji,
zuwa Dutse na Isra’ila.
30 Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja
ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa
tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa,
gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.
31 Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya
da sandar mulkinsa zai kashe su.
32 Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu
da bulalarsa na hukunci
zai zama kiɗi ga ganguna da garaya,
yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa.
33 An riga an shirya wurin ƙonawa;
an shirya shi saboda sarki.
An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi,
da isashen wuta da itacen wuta;
numfashin Ubangiji,
yana kamar kibiritu mai ƙuna,
da aka sa masa wuta.