2
Isra’ila ya yashe Allah
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Tafi ka yi shela a kunnuwar Urushalima cewa,
“ ‘Na tuna da amincin ƙuruciyarki,
yadda kamar amarya kika ƙaunace ni
kika kuma bi ni cikin hamada,
cikin ƙasar da ba a yi shuka ba.
Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji,
nunan fari na girbinsa;
dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi,
masifa kuwa ta same su,’ ”
in ji Ubangiji.
 
Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub,
dukanku zuriyar gidan Isra’ila.
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi,
da suka tsaya nesa da ni?
Sun bi gumakan banza
su kansu suka kuma zama banza da kansu.
Ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji,
wanda ya fitar da su daga Masar
ya bishe su cikin jeji
cikin hamada da kwazazzabai
ƙasa mai fări da kuma duhu,
ƙasar da ba kowa mai ratsa ta ba kowa kuma mai zama a cikinta?’
Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarka
don ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa.
Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasata
kuka kuma mai da gādona abin ƙyama.
Firistoci ba su yi tambaya,
‘Ina Ubangiji ba.’
Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba;
shugabanni suka yi mini tawaye.
Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al,
suna bin gumakan banza.
 
“Saboda haka ina sāke tuhumarku,”
in ji Ubangiji.
“Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku.
10 Ku ƙetare zuwa tsibiran Kittim* Wato, Saifurus da tsibiran wajen yamma ku gani,
ku aika zuwa Kedar ku duba da kyau;
ku ga ko an taɓa yin wani abu haka.
11 Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta?
(Duk da haka su ba alloli ba ne sam.)
Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu
da gumakan banza.
12 Ku girgiza saboda wannan, ya sammai,
ku kuma razana don tsoro mai girma,”
in ji Ubangiji.
13 “Mutanena sun aikata zunubai guda biyu.
Sun rabu da ni,
ni da nake maɓulɓular ruwan rai,
sun kuma haƙa tankunan ruwansu,
tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba.
14 Isra’ila bawa ne, bawa ne ta wurin haihuwa?
Me ya sa ya zama ganima?
15 Zakoki sun yi ruri;
sun yi masa ruri.
Sun lalatar da ƙasarsa;
an ƙone garuruwansa aka kuma watse daga ciki.
16 Haka ma, mutanen Memfis Da Ibraniyanci Nof da Tafanes
sun aske rawanin kanka Ko kuwa fasa ƙoƙon kansa
17 Ba kai ne ba ka jawo wa kanka ba
ta wurin rabuwa da Ubangiji Allahnka
sa’ad da ya bi da kai a hanya?
18 To, me ya sa za ka Masar
don shan ruwa daga Shihor?§ Wato, reshen Nilu
Kuma me ya sa za ka Assuriya
don shan ruwa daga Kogi?* Wato, Yuferites
19 Muguntarka za tă hukunta ka;
jan bayanka zai tsawata maka.
Sai ka lura ka kuma gane
yaya mugu da kuma ɗaci suke a gare ka
sa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnka
kuma ba ka tsorona,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
 
20 “Tun da daɗewa ka karya karkiyarka
ka kuma tsintsinke sarƙoƙinka;
sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’
Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayi
da kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itace
ka kwanta kamar karuwa.
21 Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi
iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai.
Yaya kuma ka juya kana gāba da ni
ka lalace, ka zama inabin jeji?
22 Ko da yake ka wanke kanka da sabulu
ka yi amfani da sabulu mai yawa,
duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,”
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
 
23 “Yaya za ka ce, ‘Ban ƙazantu ba;
ban bi Ba’al ba’?
Duba yadda ka yi a cikin kwari;
ka ga abin da ka yi.
Kai kamar makwaɗaciyar raƙuma ce mai zafin gudu
kana gudu nan da can,
24 kamar jakar jejin da ta saba da hamada,
mai busar iska cikin son barbaranta
sa’ad da take son barbara wa zai iya hana ta?
Jakin da yake nemanta, ba ya bukatar wahalar da kansa;
a lokacin barbara za a same ta.
25 Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma
maƙogwaronka kuma ya bushe.
Amma sai ka ce, ‘Ba amfani!
Ina ƙaunar baƙin alloli
kuma dole in bi su.’
 
26 “Kamar yadda akan kunyatar da ɓarawo sa’ad da aka kama shi,
haka gidan Isra’ila zai sha kunya,
su, sarakunansu da shugabanninsu,
firistocinsu da kuma annabawansu.
27 Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’
ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’
Sun juye mini bayansu
ba fuskokinsu ba;
duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce,
‘Zo ka cece mu!’
28 To ina allolin da kuka yi wa kanku?
Bari su zo in suna iya cetonku
sa’ad da kuke cikin wahala!
Gama kuna da alloli masu yawa
kamar yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda.
 
29 “Me ya sa kuke tuhumana?
Dukanku kun yi mini tawaye,”
in ji Ubangiji.
30 “A banza na hukunta mutanenku;
ba su yi gyara ba.
Takobinku ya cinye annabawanku
kamar zaki mai jin yunwa.
31 “Ku na wannan zamani, ku saurari maganar Ubangiji.
“Na zama wa Isra’ila hamada ne
ko ƙasa mai babban duhu?
Me ya sa mutanena suke cewa, ‘Muna da ’yanci mu yi ta yawo;
ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
32 Budurwa za tă manta da kayan adonta
amarya ta manta da kayan adon aurenta?
Duk da haka mutanena sun manta da ni,
kwanaki ba iyaka.
33 Kuna da azanci sosai a bin masoya!
Kai, ko mafiya muni cikin mata tana iya koya daga hanyoyinku.
34 A rigunanku mutane kan sami
jinin matalauta marasa laifi,
ko da yake ba ku kama su suna fasawa su shiga ba.
Duk da haka
35 kuna cewa, ‘Ba ni da laifi;
ba ya fushi da ni.’
Amma zan zartar da hukunci a kanku
domin kun ce, ‘Ban yi zunubi ba.’
36 Don me kuke yawo da yawa haka,
kuna ta canjin hanyoyinku?
Masar za tă kunyata ku
yadda kuka sha kunya a wurin Assuriya.
37 Za ku kuma bar wurin
da hannuwanku a kanku,
gama Ubangiji ya ƙi waɗanda kuka amince da su;
ba za ku zama abin taimako a gare su ba.
 
 

*2:10 Wato, Saifurus da tsibiran wajen yamma

2:16 Da Ibraniyanci Nof

2:16 Ko kuwa fasa ƙoƙon kansa

§2:18 Wato, reshen Nilu

*2:18 Wato, Yuferites