19
An yanke wa Yesu hukuncin mutuwar gicciye
1 Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. 2 Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. 3 Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
4 Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.” 5 Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”
6 Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!”
Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
7 Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
8 Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, 9 sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10 Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
11 Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
12 Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”
13 Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). 14 Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida.
Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”
15 Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!”
Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?”
Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
16 A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi.
Gicciyewa
Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu. 17 Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). 18 Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
19 Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne,
Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.
20 Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. 21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”
22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”
23 Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.
24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.”
Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce,
“Suka rarraba tufafina a junansu,
suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.”* Zab 22.18
Abin da sojojin suka yi ke nan.
25 To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26 Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27 ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Mutuwar Yesu
28 Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29 To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu. 30 Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
31 To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan. 32 Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan. 33 Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. 34 A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito. 35 Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata. 36 Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,”† Fit 12.46; Ƙid 9.12; Zab 34.20 37 kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
Jana’izar Yesu
38 Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin. 39 Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari. 40 Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza. 41 A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba. 42 Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.