10
Yesu ya aiki saba’in da biyu
1 Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. 2 Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa. 3 Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai. 4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.
5 “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’ 6 In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku. 7 Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida.
8 “Sa’ad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku. 9 Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’ 10 Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce, 11 ‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’ 12 Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.
13 “ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka. 14 A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku. 15 Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki.
16 “Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”
17 Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”
18 Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya. 19 Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. 20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”
21 A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.
22 “Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.”
23 Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani. 24 Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”
Misalin mutumin Samariya nagari
25 Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
26 Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”
27 Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”
28 Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”
29 Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”
30 Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. 31 Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa. 32 Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa. 33 Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. 34 Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. 35 Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’
36 “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”
37 Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.”
Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”
A gidan Marta da Maryamu
38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”
41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”