18
Mafi girma a mulkin sama
1 A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?”
2 Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. 3 Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4 Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5 Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.
6 “Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku. 7 Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su! 8 In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu. 9 In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.
Misalin ɓatacciyar tunkiya
10 “Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.* Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da sama. 11 Ɗan Mutum ya zo ne domin yă ceci abin da ya ɓata
12 “Me kuka gani? In wani yana da tumaki ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓace, ba sai yă bar tasa’in da taran a kan tuddai yă je neman guda ɗayan da ta ɓace ba? 13 In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasa’in da taran da ba su ɓace ba. 14 Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yă ɓace.
Ɗan’uwa da ya yi maka laifi
15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. 16 Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’† M Sh 19.15 17 In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.
18 “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.
19 “Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku. 20 Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”
Misalin bawa marar tausayi
21 Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”
22 Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.‡ Ko kuwa saba’in sau bakwai
23 “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. 24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma. 25 Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.
26 “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ 27 Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.
28 “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’
29 “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’
30 “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin. 31 Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.
32 “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. 33 Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ 34 Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.
35 “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”