6
Damuwar Ubangiji a kan Isra’ila
1 Ku saurari abin da Ubangiji ya ce,
“Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu;
bari tuddai su ji abin da kuke so ku faɗa.
2 “Ku saurara, ya ku duwatsu game da tuhumar da Ubangiji yake muku,
ku ji, ku daɗaɗɗun tushin duniya.
Gama Ubangiji yana da ƙara a kan mutanensa;
yana tuhumar Isra’ila.
3 “Ya ku mutanena, me na yi muku?
Ta yaya na nawaita muku? Ku amsa mini.
4 Na fito da ku daga ƙasar Masar
na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta.
Na aika da Musa yă jagorance ku,
haka ma Haruna da Miriyam.
5 Ya ku mutanena, ku tuna
abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla
da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar.
Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal,
don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”
6 Da me zan zo a gaban Ubangiji
in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah?
Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa,
da ɗan maraƙi bana ɗaya?
7 Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai
da kuma rafuffukan mai dubbai goma?
Zan ba da ɗan farina ne don laifina,
ko ’ya’yan jikina domin zunubin raina?
8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.
Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa
shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai
ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
Laifin Isra’ila da kuma hukunci
9 Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni,
a ji tsoron sunana kuwa hikima ce,
“Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa.* Ma’anar Ibraniyanci na wannan layin babu tabbas.
10 Har yanzu zan manta, ya muguwar gida
da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya
zan kuma manta da bugaggen mudun awo† Efa mudun awo ne na busasshen abu. wanda ake zargi?
11 Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya,
da kuma buhun ma’aunan ƙarya?
12 Attajiranta masu fitina ne;
mutanenta kuma maƙaryata ne
harsunansu kuwa suna yaudara.
13 Saboda haka, zan hallaka ku
in lalace ku saboda zunubanku.
14 Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba,
cikinku zai zama babu kome‡ Ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma babu tabbas.
Za ku tattara amma ba za ku yi ajiyar kome ba,
gama abin da kuka yi ajiya zan ba wa takobi.
15 Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba;
za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba,
za ku tattaka ’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.
16 Kuna kiyaye ƙa’idodin Omri
da dukan ayyukan gidan Ahab
kun kuma bi al’adunsu.
Saboda haka, zan maishe ku kufai
in mai da ku abin dariya a cikin mutane,
za ku sha reni a wurin al’ummai.”§ Seftuwajin; da Ibraniyanci suna da abin zargi ga mutanena ne a nan