6
Annabi marar daraja
1 Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa. 2 Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki.
Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka! 3 Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.
4 Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.” 5 Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su. 6 Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu.
Yesu ya aiki sha biyun
Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa. 7 Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.
8 Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. 9 Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa. 10 Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin. 11 In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”
12 Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba. 13 Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.
An yanke kan Yohanna Mai Baftisma
14 Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”
15 Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.”
Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.”
16 Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!”
17 Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura. 18 Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.” 19 Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba, 20 domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi.
21 A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. 22 Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa.
Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.” 23 Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”
24 Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?”
Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.”
25 Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.”
26 Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba. 27 Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. 28 Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta. 29 Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari.
Yesu ya ciyar da dubu biyar
30 Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar. 31 To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”
32 Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa. 33 Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can. 34 Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.
35 A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure. 36 Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”
37 Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.”
Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum!* Girik zai ci dinari ɗari biyu Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”
38 Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.”
Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”
39 Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. 40 Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. 41 Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. 42 Kowa ya ci, ya ƙoshi, 43 almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. 44 Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.
Yesu ya yi tafiya kan ruwa
45 Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron. 46 Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.
47 Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai. 48 Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49 amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50 domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.
Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” 51 Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, 52 gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.
53 Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya. 54 Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu. 55 Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake. 56 Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.