11
Shiga mai nasara
1 Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa, 2 ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan. 3 In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ”
4 Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan, 5 sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?” 6 Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su. 7 Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa. 8 Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki. 9 Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa,
“Hosanna!* Wani faɗi ne na Ibraniyanci mai ma’ana “Ceto!” Wanda ya zama kalmar yabo; haka ma a aya 10”
“Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”† Zab 118.25; Zab 118.26
10 “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!”
“Hosanna a can cikin samaniya!”
11 Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
Yesu ya tsabtacce haikali
12 Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa. 13 Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. 14 Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.
15 Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, 16 ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. 17 Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’?‡ Ish 56.7Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’§ Irm 7.11”
18 Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
19 Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka* Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ya bar garin.
Itacen ɓaure da ya yanƙwane
20 Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. 21 Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
22 Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah. 23 Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. 24 Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku. 25 A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”† Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da zunubai. 26 Amma idan ba kwa yafewa, Ubanku ma da yake sama, ba zai yafe muku zunubanku ba.
An tuhumi ikon Yesu
27 Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa. 28 Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
29 Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. 30 Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!”
31 Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 32 In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.”
33 Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”
Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”
*11:9 Wani faɗi ne na Ibraniyanci mai ma’ana “Ceto!” Wanda ya zama kalmar yabo; haka ma a aya 10
†11:9 Zab 118.25; Zab 118.26
‡11:17 Ish 56.7
§11:17 Irm 7.11
*11:19 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ya
†11:25 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da zunubai. 26 Amma idan ba kwa yafewa, Ubanku ma da yake sama, ba zai yafe muku zunubanku ba.