12
Misalin ’yan haya
1 Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya. 2 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu. 3 Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. 4 Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi. 5 Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.
6 “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’
7 “Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’ 8 Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.
9 “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan ’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin. 10 Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba,
“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,
shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.
11 Ubangiji ya yi wannan,
ya kuma yi kyau a idanunmu’?”* Zab 118.22,23
12 Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu.
Biyan haraji ga Kaisar
13 Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa. 14 Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? 15 Mu biya ko kada mu biya?”
Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.” 16 Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?”
Suka ce, “Na Kaisar.”
17 Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.”
Suka yi mamakinsa ƙwarai.
Aure a tashin matattu
18 Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya. 19 Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya. 20 To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya. 21 Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun. 22 A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu. 23 To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”
24 Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah? 25 Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama. 26 Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?† Fit 3.6 27 Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”
Dokar da ta fi girma duka
28 Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”
29 Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30 Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’‡ M Sh 6.4,5 31 Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’§ Fir 19.18Ba wata doka da ta fi waɗannan.”
32 Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. 33 Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”
34 Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.
Kiristi ɗan wane ne?
35 Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne? 36 Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana
sai na sa abokan gābanka
a ƙarƙashin sawunka.” ’* Zab 110.1
37 Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?”
Taro mai yawa suka saurare shi da murna.
38 Sa’ad da Yesu yake koyarwa ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci. 39 Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majami’u, da kuma wuraren zaman manya a bukukkuwa. 40 Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen addu’o’i. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.”
Bayarwar gwauruwa
41 Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. 42 Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo.
43 Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan. 44 Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.”